RASHA 2018: Faransa ta haddasa wa Peru yin sammakon-bubukuwa

0

Faransa ta yi wa Peru ci daya mai ban-haushi, wanda ya sa a zaman yanzu ko da ta ci wasan ta na gaba, to Peru gida za ta koma.

Kasar Peru dai na daga cikin kasashen da suka je gasar da wuri, kuma ta na cikin kasashen da za su koma gida da wuri.

Dan wasan PSG, Kylian Mbappe ne ya ci wa Faransa kwallo daya, wanda ya kafa tarihin cewa shi ne dan wasa mafi karancin shekaru da ya taba ci wa Faransa kwallo a shekara 19 da haihuwa.

Duk da Peru ta samu damar cin kwallaye, hakan bai ba ta sa’ar jefa ko kwallo daya ba har aka tashi wasan.

Duk da cewa Paul Pogba bai ci kwallo ba, amma a gaskiya shi ne kashin-bayan nasarar da Faransa ta samu a gasar, idan aka yi la’akari da irin bajintar da ya nuna a wasan yau.

Share.

game da Author