RASHA 2018: Denmark ta raba maki da Australia

0

Dan wasan Australia ya karya rekod din mai tsaron gida Scheimichel na Denmark, wanda ya buga wasa hudu a jere ba tare da an saka masa kwallo ko daya a raga ba.

An jefa masa kwallon ne a wasan su daidai minti na 38 da fara wasa a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan dan wasan Denmark ya taba kwallo a cikin yadi 18.

Kafin nan kuwa, Denmark din ce ta fara cefa kwallo a daidai minti na 7 da fara wasan su.

Dan wasa Jorgensen ne ya shandamo wa Ericksen kwallo ta sama, inda shi kuma bai yi wata-wata ba, sai ya fantsama ta cikin ragar Autralia.

An yi tsammani Australia za ta yi kokarin yin nasara, ganin yadda aka yi ha-maza-ha-mata tsakanin ta da Faransa, kafin Faransa ta yi galaba a kan ta da ci 2:1 a wasan su na farko a gasar cikin makon da ya gabata.

Kafin wannan wasa, Denmark ta yi nasara a kan Peru da ci daya mai ban-haushi.

Yanzu kenan Denmark ta fara jin kamshin shiga zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya da ka yi a Rasha.

Amma idan Australia ta yi nasara a kan Peru, daga nan za a sake tantance cewa ba a san maci tuwo ba tukunna, har sai miya ta kare.

Mai tsaron gidan Australia ya yi namijin kokarin da ya hana kwallo shiga ragar su har kusan sau goma, bayan cin farko da aka yi masa.

Share.

game da Author