Mahaifiyar shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau, Malama Falmata Abubakar ta bayyana cewa a yanzu haka bata da masaniyar halin da ‘dan ta Abubakar Shekau ya ke ciki.
Kamar yadda VOA Hausa ta ruwaito, Falmata dai mazauniyar garin Shekau ne dake jihar Yobe, wanda wannan shine karo na farko da zata yi magana kan dan ta kuma shugaban Boko Haram Abubakar Shekau.
Mutanen garin Shekau sukan boye jibanta kan su da garin saboda kada a rika yi musu lakani da wannan suna.
” Rabon da in hada ido da da na Abubakar Shekau ya fi shekaru 15. ko yana raya ko ya mutu, Allah kadai ne ya sani.
Falmata ta kara da cewa tun bayan tafiyarsa karatun almajiranci garin Maiduguri, a nan ne ya hadu da shugaban kungiyar Boko Haram a wancan lokaci wato Mohammed Yusuf. Daga nan ne fa ya dulmiya akidar Boko Haram.
” Shekau ‘da na ne kuma kowa ce uwa na son danta amma dai na sani hanyar sa da bam da namu. Ya saka mutane a kasar nan cikin matsanan cin hali matuka, roko na dai Allah ya shirya shi.
Ta ce ita baza ta tsine wa dan ta ba amma kam ya zabi hanyar da ba ita bace muka saka shi akai wanda Allah ne kadai yasan irin abin da ya zama yanzu.
Mahaifin Shekau limamin garin su a wancan lokaci kuma ya dade da rasuwa.