Hon Kawu Sumaila ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa shi da kan sa ya gaya wa tsohon gwamnan jihar Kano Rabiu Kwankwaso cewa kada ya yi karfa-karfa wajen dora dan takara ba tare da an bi yadda doka ta gindaya ba amma akayi watsi da wannan shawara tasa, gwamnan ya dora wanda yake so.
“ Ina so in gaya muka ka sani, wannan magana na yi ta nanata shi. Lokacin da aka kafa APC na bada shawarar a tabbata an bi doka wajen dora shugabannin jam’iyya da zaben ‘yan takara. Amma maimakon abi wannan shawara sai aka koma aka ci gaba da yadda dama can ake yi a jam’iyyar PDP, jiya Iyau tun da dama can mun sani ba zai hafi da mai ido ba.
“ Haka akayi a lokacin zaben fidda dan takara, gwamnoni suka dora wadanda suke so, akayi watsi da yadda dokar jam’iyya tace abi ba.
” A lokacin na jawo hankalin gwamna Kwankwaso cewa ya bi doka, kada yace zai ba na kusa dashi amma ya ki ji na. Na ce masa idan ya dora na kusa dashi, ba za a sami dasawa ba.
” A wancan lokaci har Ina ba da misali da yadda ta kaya tsakanin wasu gwamnoni da suka yi irin haka amma ba a gama lafiya ba kamar Aliero da Dakingari, Ali Saadu Da Sule Lamido, Saminu Turaki Da Sule Lamido da dai sauran su. Dama mun yi wannan hasashen kuma hakan ya faru.
Hon Sumaila ya kara dacewa duk da wannan matsala da aka samu, shi yana tare da gwamman jihar Kano ne wato Abdullahi Ganduje ba Kwankwaso ba.
“ Yanzu kam Ina tare ne da Ganduje saboda yana tare da Buhari. Amma fa Buhari ne ya hada mu. Kaunar da yake wa Buhari shine yasa nima nake kaunar sa. Dama can tare ya zo ya same mu tun a lokacin da baya yin Buhari har yazo yana yin sa yanzu kaga dole muna tare kenanan.
Da yake amsa tambayar ko ficewar kwankwaso a APC zai iya yi wa jam’iyyar Illa, sai yace tabbas rasa dan siyasa a jam’iyya ya kan yi wa jam’iyya Illa tunda ita siyasa da yawanku ne kuke cin zabe, saboda haka kowa so yake ya samu karuwar mutane ba raguwa ba.