Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Filato Kunden Deyin ya bayyana cewa mutane uku sun kamu da cutar Kwalara a jihar.
Ya fadi haka ne da yake zantawa da manema labarai a Jos ranar Litini.
Deyin yace da farko sun dauka mutane 93 ne suka kamu da cutar, sai dai kuma bayan gwaji da suka yi sai suka gano mutane uku ne kawai suka kamu da cutar.
Ya ce za a ci gaba da wayar wa mutanen jihar domin ganin cewa cutar bai ci gaba da yaduwa ba, sannan kuma ya hori mutanen garin da su maida hankali wajen tsaftace muhallin su.