Mutane sama da 500,000 ake bindige duk shekara a duniya-UN

0

Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta gudanar, ya nuna cewa a duk shekara ana bindige sama da mutane dubu 500 a duniya ta hanyar amfani da kananan bindigogi da suka hada da libarba, fistol, raful, mashing da sauran kananan bindigogi.

Shugaban Majalisa na Majalisar Dinkin Duniya, Maria Viotti ce ta bayyana haka, ta na mai cewa kananan bindigogi da matsakaitan bindigogi su na tsintar kan su a filayen yaki da kuma kan titinan biranen cikin duniya, inda ake tafka aika-aika da su.

Ta ce wadannan makamai kuwa babbar barazana ce a duniya baki daya.

Wakilan gwamnatocin kasashen duniya na taro a Hedikwatar Majalisar Dinkin Duniya, domin a samu kan yadda za a magance ambaliyar kanana da matsakaitan makamai a hannun jama’a a duniya.

Binciken dai ya nuna cewa akwai sama da makamai biliyan daya da ke hannayen jama’a a duniya. Ya ce ciki har da wasu miliyan 857 da ke hannun fararen hula a duniya.

Amurkawa maza da mata, su ke rike da kashi 50 bisa 100 na kananan makaman da ke hannun farafen hula.

Share.

game da Author