Kungiyar likitoci na Najeriya (NMA) ta yi kira ga gwamnati da kotun (NIC) da ta bata damar tsoma baki cikin zama da za ayi don tattauna batun biyan bukatun kungiyar ma’aikatan asibitocin kasar nan, (JOHESU).
Kungiyar NMA ta ce saka ta cikin tattaunawar zai sa a samu daidaituwa da samun maslaha a tsakanin su duka biyun da suka jani-in-jaka wajen nuna fifiko da dabur-dabur din da ya damalmale fannin kiwon lafiya a kasar nan.
” A matsayin mu Likitoci wato shugabanin fannin kiwon lafiya kamata yayi mu hada hannu don ganin fannin ta ci gaba sannan saka baki cikin tattaunawar zai samar da zaman lafiya a tsakanin ma’aikatan.