Matakan Tsige Shugaban Kasa a Dokar Najeriya

0

Mataki Na 1

Tashin farko sai an samu akalla kashi 1 bisa 3 na Sanatoci da mambobin Majalisar Tarayya kowanen su ya sa hannu a kan jerin laifukan da suke tukumar Shugaban Kasa da su. Sannan sai su aika wa Shugaban Majalisar Dattawa wasikar bukatar su ta neman tsige shugaban tare da kwafen takardar da ke dauke da laifukan da ya aikta.

* LAIFIN SHUGABA: Kamar yadda dokar Najeriya ta gindaya, “ya kasance Shugaban Kasa ya karya wasu dokoki na Najeriya a wajen tafiyar da mulkin sa, ko kuma wani abu na ba daidai ba wanda majalisar ta gamsu da cewa ya aikata ba daidai ba.

Mataki Na 2

Tilas ya kasance cikin kwana bakwai Shugaban Majalisar Dattawa ya aika wa Shugaban Kasa da kowane Dan Majalisa da Sanata da kuma Shugaban Kasa kwafen wasikar, wacce ke dauke da zarg-argen tuhumar da ake yi masa.

Mataki Na 3

Shugaban Kasa na da damar maida musu da amsa, ko kuma ba sai ya maida musu da amsa ba, duk daya. Amma idan har zai maida amsa, to ya kasance tilas wasikar ta isa ga dukkan Sanatoci da ‘yan Majalisar tarayya.

Mataki Na 4

A cikin kwanaki 14 da karbar takardar neman tsige Shugaban Kasa, zai kasance Majalisar Tarayya da Majalisar Dattawa sun yi zama a majalisar su domin su amince da cewa shin akwai bukatar a binciki zargin ko kuwa? Sai akalla kashi 2 bisa 3 na mambobin sun amince tukunna.

Mataki Na 5

Idan har yunkurin ya kasa samar da adadin yawan ‘yan majalisar da za su goyi bayan sa, to sai nan da nan a dakatar da yunkurin tsigewar. Ba za a sake daukar wani mataki ba. Amma idan an samu yawan adadin da akalla ake bukata na masu son a tsige shugaban ya kai yadda doka ta gindaya, to a cikin kwana bakwai da amincewa sai Shugaban Majalisar Dattawa ya umarci Babban Cif Joji na Tarayya ya kafa kwamiti na mutane 7, wadanda ya ke ganin cewa mutane ne masu gaskiya, amana kuma wadanda ake kyautata wa adalci domin su bincki zarge-zargen da Majalisa ta yi wa Shugaban Kasa.

Sannan kuma ya kasance daga cikin mambobin babu ma’aikacin gwamnati kuma babu dan majalisar dattawa ko ta tarayya.

Mataki Na 6

Ya kasance kwamitin bincike ya bayar da sakamakon binciken da ya yi a cikin watanni uku. Za su bada sakamakon binciken ga Majalisar Dattawa da ta Tarayya.

A lokacin da kwamitin ke binciken sa, Shugaban Kasa na da damar kare kan sa, kuma ya na da damar da zai tura lauyan sa ya kare shi a madadin sa.

Mataki Na 7

Idan kwamitin bincike ya bada rahoton cewa ba a kama Shugaban Kasa da tafka laifi ba, to ba za a kara daukar wani mataki ba. Amma idan kwamitin bincke ya kama Shugaban Kasa da laifi, sai Majalisa su amince da rahoton, sannan su dauki haramar zartas da kudirin tsige shi.

Mataki Na 8

Sai kashi 2 bisa 3 na Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya sun amince a tsige shugaban kasa sannan za a ce ya tsigu.

Share.

game da Author