Makarantu za mu gina a matattarar mashaya da karuwai na unguwar Galadima- Gwamna Kashim

0

Gwamnatin jihar Barno ta sanar cewa za ta gina makarantu ne a matattaran karuwai da mashayar muggan kwayoyi dake unguwar Galadima a Maduguri.

Gwamnatin jihar ta kafa kwamiti da zai jagoranci tasa, rusawa da gina makarantun a wadannan wurare dake unguwar.

Gwamnan jihar Kashim Shettima ne ya fadi haka da ya kai ziyarar gani da ido wannan unguwa na Galadima.

Da yake jinjina wa kwamitin kan ayyukan da ta gudanar zuwa yanzu Shettima ya ce wadanda suke da cikakkun takardun filayen su a wurin ba za a tada su ba amma duk wanda bai da takardun mallakar fili a wannan wuri, za a tada shi.

Ya ce gwamnati ba za ta sa ido ta bari muggan ayyuka irin shaye-shaye da sana’ar karuwanci yayi wa jihar Katutu ba.

” Dole gwamnati ta kawar da ire-iren wadannan unguwanni a jihar domin gujewa fadawa matsaloli da jihar ta fuskanta kamar su Boko Haram da sauran su.

Share.

game da Author