Mahara sun kashe daliban jami’a biyu a Katsina

0

Wasu mahara sun kashe daliban jami’a biyu a kauyen Bagiwa da ke cikin Karamar Hukumar Mani a Jihar Katsina.

Harin, wanda su ka kai da saiyar Lahadi, sun kashe daliban ne wadanda ke karatu a Jami’ar Al-Qalam ta Katsina, kuma suka ji wa mahaifiyar su mai shekaru 60 a duniya rauni.

An kuma tabbatar da cewa sun yi garkuwa da mutum daya a garin.

Ibrahim Bature ya na matakin ‘400 Level’ ne, yayin da Rabi’u Abubakar kuma mai shekaru 21, ya na matakin karatu na ‘200 Level.’

Mai magana da yawun iyalan mamatan, Lawal Bagiwa, ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN cewa maharani sun yi garkuwa da yayan daliban, mai suna Umar.

Ya ce maharani sun kutsa cikin gidan, inda suka rika yin harbin-kai-mai-uwa-da-wabi, ba tare da neman a ba su komai ba.

Har yanzu kuma ba a tabbatar da inda suke ba.

Kakakin ‘yan sandan Katsina Isa Gambo, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce su na ci gaba da bincike.

Share.

game da Author