Kwamishinan kiwon lafiya na jihar Gombe Kennedy Ishaya ya sanar cewa cutar kwalara ta bullo a makarantar lslamiya dake Madaki a jihar.
Ishaya ya bayyana cewa a dalilin haka dalibai uku sun rasa rasu sannan 27 na kwance a cibiyar kiwon lafiya dake Madaki.
” A cikin kwanaki uku daliban makarantar wannan Islamiya 30 sun kamu da cutar sannan daga ciki uku suka rasu.
” A yanzu haka asibitin ta sallami dalibai 15 sannan ana ci gaba da kula da sauran 12.
Ishaya ya yi kira ga mutane da su gaggauta zuwa asibiti a duk lokacin da wani ya kamu da rashin lafiya ko kuma aka alamun haka cewa gwamnati ta zuba magani a asibitocin jihar.
” Sannan a tabbatar an yi amfani da tsaftatacen ruwa musamman a lokacin yin alwala domin guje wa kamuwa da cutar.
A karshe yi kira ga malaman asibiti da su kare kansu daga kamuwa da cutar suma.