Kotu ta yanke wa wasu masu garkuwa da mutane hukuncin kisa ta hanyar rataya

0

Kotu dake zama a garin Yola, jihar Adamawa ta yanke wa mutane hudu hukuncin kisa bayan ta kama su da laifin yin garkuwa da mutane da ayyukan fashi da makami.

Alkalin kotun Abdul-Azeez ya yanke wa Gambo Musa, Mana Musa, Abdu Baba da Mohammed Muazu hukuncin kisa ta hanyar rataya ko kuma kisa ta hanyar harbi da bindiga saboda kama su da laifin aikata wadannan laifuka.

Bayan haka kafin a kashe ta hanyar rataya din a hukuncin da aka yanke, sai sun yi zaman wakafi na shekaru 10 tukunna saboda sace dan majalisa Taungo Adamu Usman da wani ma’aikacin gwamnati Wilson Gundiri.

Sai dai kuma a lokacin da kotun ta yanke wa wadannan mutane wannan hukunci dukan su sun riga sun mutu yayin da suke tsare a kurkuku.

Bayan wadannan mutane da aka yanke wa wannan hukunci, kotun ta sake yanke wa wasu mutane biyar hukuncin kisa bayan kama su da tayi da laifin kisa da suka aikata kan wani fulani makiyayi da sace masa shanu masu yawa.

” Bincike ya nuna cewa bayan wadannan mutane sun kashe makiyayin sai suka jefar da gawar sa a rafin kauyen Kadomon.” Inji Kotu.

Wadanda aka yanke wa hukuncin kisan sun hada da Alex Amos, Alheri Phanuel, Holy Boniface, Jerry Gideon da Jari Sabagi.

Share.

game da Author