Kotu ta tsare mutane hudu bayan sun kashe abokin su, sun cire cire zuciyar sa

0

Kotun Majistare da ke unguwar Yaba, cikin birnin Legas, ta tsare wasu mutane hudu da ake zargi da laifin kashe abokin aikin su, sannan kuma suka cire zuciyar sa suka yi tsafi da ita.

Wadanda aka tsare din su ne Daniel Luka, Audu Isaiah, Wavi David da kuma Ayuba Musa.

Ana zargin su da laifi biyu, wato hadin baki a tsakanin su tare da aikata laifin kisa.

Mai gabatar da kara Modupe Olaluwoye, ta shaida wa kotu cewa mutanen hudu sun aikata kisan ne a ranar 22 Ga Mayu, a Alasia, kan hanyar Ajah, kusa da Legas.

Olaluwoye ta kara da cewa su hudun sun yi kaurin suna wajen zuwa wurin matsafi, wanda shi matsafin ya nemi su kai masa zuciyr mutum domin yay i musu asirin da za su zama hamshakan attajirai.

Ta kara da cewa su hudun sun yaudari abokin aikin su mai suna James Isaiah, suka tafi cikin jeji, daga can nuka kashe shi ta hanyar yin amfani da wuka, bayan nan kuma suka hatarta shi,

“Yan sanda sun ritsa su a cikin gidan su, inda suka fada da kan su cewa su ne suka kashe dan uwan na su domin su yi tsafi da zuciyar sa.

“Har yanzu ana neman matsafin an rasa, tuni jin cewa an cafke kwastomomin sa hudu, sai shi kuma ya cika rigar sa da iska.”

Share.

game da Author