Kotu ta hana Shekarau zuwa Umra

0

Mai Shari’a Zainab Bage Abubakar ta Babbar Kotun Tarayya a Kano, ta ki amincewa da rokon da Tsohon Gwmnan Jihar, Ibrahim Shekarau ya yi mata a rubuce, na neman amincewa ya je aikin Umra a Saudi Arabiya.

Shekarau ya rubuta wa kotun takardar sanar da ita, inda ya roki mataimakin magatakardar kotun da ya ba shi fasfo din sa, domin ya je Umra.

Ya rubuta takardar ce a ranar 28 Ga Mayu, 2018, inda ya ce zai tafi a ranar 30 Ga Mayu, sannan ya dawo a ranar 23 Ga Mayu.

Yayin da aka koma sauraren ba’asi a Jiya Talata a kotun, lauyan Shekarau, mai suna Abdul Adamu, ya gabatar da wasikar da aka rubuta, sai dai kuma mai gabatar da kara Johnson Ojogbane ya gabatar da wata takarda mai dauke da rubutu shafuka 9, inda ya roki kotun cewa kada a bar Shekarau ya fita zuwa kasar waje.

Mai Shari’a Zainab ta ce ba dole ba ne kuma bai kamata a ba Shekarau fasfo din sa ba, domin a cikin sharuddan bayar da belin sa, har da cewa sai ya ajiye fasfo din sa a kotun tukunna.

A bisa wadannan dalilai ne ta ki bada umarni a ba shi fasfo din domin ya fita zuwa Umra.

Share.

game da Author