Kotu ta daure wani matashi da ya yi wa ‘yar shekara tara fyade a Kaduna

0

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, ta gurfanar da wani matashi dake sana’ar tireda dan shekaru 19 a kotun dake titin Daura a garin na Kaduna kan Zargin aikata fyade da yayi wa wata ‘yar shekara 9.

Ofishin ‘yan sanda da ke unguwar Rigasa ne suka shigar da kara.

Dan sandan da ya shigar da karan Hinga Nyimze ya bayyana a kotun cewa matashin mai suna Lawal Daura mazaunnin ‘Yan kifi ne a unguwar Rigasa sannan ya aikata wannan ta’asa ne ranar biyu ga watan Yuni amma ba a shigar da kara ba sai ranar 19 ga watan Yuni.

” Shi dai wannan matashi mai suna Daura ya faki lokacin da yarinyar take dawowa ne daga makarantar Islamiya, daganan sai ya lallabeta suka shiga dakin sa. Anan ne fa ya aikata lalata da ita da karfin tsiya.

” Ita kuwa yarinya ficewar ta daga dakin Daura ke da wuya sai ta falla sai gaban iyayen ta inda ta kwashe labarin abinda ya faru tsakanin ta da shi wato Daura dalla-dalla.

Nyimze ya ce Daura dai ya masa laifin sa karara.

A karshe alkalin kotun Abdulaziz Ibrahim ya yi watsi da rokon sassaucin da Daura ya yi sannan ya yanke hukuncin daure shi a kurkuku har sai ya kammala yin shawara da hukumar gurfanar da masu aikata laifuka irin haka a jihar.

Za a ci gaba da shari’ar ranar biyu ga watan Agusta.

Share.

game da Author