Ko ka san yin tafiya da sauri na kara lafiya da tsawon rai?

0

Wasu likitoci a jami’ar kasar Australia sun gano cewa yin tafiya da sauri na kara lafiya da tsawon rai.

Likitocin sun gano haka ne bayan yin gwaji kan wasu mutane 50,000 da suka raba su kashi biyu.

A bayanan binciken sun nuna cewa duk masu tafiya da sauri sun fi dadewa da lafiya fiye da wadanda basu kan yawan yin tafiya ko kuma basu cika yin sauri ba. Sannan kuma hakan kan yi sauri yin ajalin mutum musamman wanda shekaru suka yi wa nisa.

Likitocin sun hori mutane da su yawaita yin tattaki da sauri saboda samun karfin kashi da lafiyar jiki.

Share.

game da Author