Kiris ya rage in hakura da mulkin Jigawa, da na ga irin harkallar da Sule Lamido ya yi da kudin jihar – Gwamna Badaru

0

Gwamnan jihar Jigawa Abubakar Badaru ya bayyana yadda basukan da ya tadda a jihar bayan rantsar da shi gwamna a 2015 ya kusa hana shi iya gudanar da mulki a jihar.

Ya ce gwamnatin baya ta bar dimbin basuka da ayyuka da basu kammala ba da suka kai Naira biliyan 31.3.

Badaru ya bayyana haka ne a gidan gwamnati dake Dutse da yake zantawa da wakilin PREMIUM TIMES game da matsalolin da ya fuskanta bayan rantsar dashi gwamnan jihar Jigawa shekaru uku da suka wuce.

Badaru ya ce tun daga shekarar 2015 da ya hau mulki a jihar ya kashe Naira biliyan 51 wurin karisa ayyuka da biyan basukan da gwamnatin baya ta bari wanda ya kai biliyan 31.3.

Ya ce gwamnatin baya ta haka masa ramin mugunta ne domin ya fada amma da taimakon Allah ya tsallake wannan makirci.

” A haka a haka dai mun samu mun iya biyan albashin ma’aikata, muna iya biyan ‘yan fansho da wasu alawus alawus din ma’aikatan jihar.

” Mun kuma bunkasa aiyukkan noma a jihar ta hanyar zuba kudade a noman siga, shinkafa da kiwon dabbobbi wanda a yanzu an samar wa mutane 30,000 aiki jihar.

” A fannin kiwon lafiya gwamnati ta ci gaba da gyara cibiyoyin kiwon lafiya a jihar da samar wa mata masu ciki da yara ‘yan kasa da shekara 5 kiwon Lafiya kyauta a fadin jihar.

” Gwamnati ta gina ajujuwa 4,520, dakunan zagawa a makarantu 411, ofisoshin malaman makarantu 6, kujerun dalibai 97,659, kujerun malamai 3,416, gidaje malamai 188, dakunan kwana na dalibai 4 da rijiyoyin burtsatsai da ya kai Naira biliyan 9.8.

Gwamna Badaru ya kuma ce yana gina dakunan kwana domin masu yi wa kasa hidima a duk kananan hukumomin jihar.

Bayanai sun nuna cewa ginin zai dauki akalla masu yi wa kasa hidima 4,000 idan dai aka kamala ginawa.

A karshe ya ki amsa tambayoyi game da fitowa takaran gwamnan jihar duk da cewa wasu ‘yan jam’iyyarsa wato APC suna yin kira garesa da ya fito takarar gwamnan jihar.

Akwai yan adawa kamar su sanata Ubale Shitu mai wakiltan Jigawa ta arewa maso yamma da wasu ‘yan jam’iyyar PDP kamar tsohon gwamnan jihar Sule Lamido da ke adawa da zaman sa gwamna a jihar kuma sun lashi takobin ganin bai koma kujerar gwamna a jihar ba ko da ya nemi ta zarce.

Share.

game da Author