Jakadan Najeriya a Saudiyya, Isa Dodo, ya karyata zargin da wasu ke yi cewa da hadin bakin sa ake safarar mata daga Najeriya ana kai su Saudiyya su na yin aikatau.
Dodo ya karyata wannan zargi ne a wata hira da aka yi da shi a Kamfanin Dillancin Labarai, NAN, a ranar Labara.
Ya ce babu ruwan Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya da kuma kuma hi kansa da ofishin sa a harkallar kai mata masu aikatau zuwa Saudiyya.
“Na samu labarin wasu ejan na Najeriya su na safarar mata su kai su Saudiyya suna aikatau a gidaje sun a yin aikatau.
Ya ce masu yin wannan harkallar su na yi ne ba tare da sanin Ma’aikatar Harkokin Waje a Abuja ba, ko kuma ofishin sa da ke Riyad, Saudi Arabia.
Yayin da ya ke jan hankalin jama’a, ya kara da cewa an ce tun sama da shekara uku ake wannan safarar mata, to amma shi watan sa bakwai kadai da akama aiki.