Babban dan tsohon hamshakin attajirin nan kuma wanda ake da yakinin shine ya lashe zaben 1993, Kola Abiola ya bayyana cewa yayi matukar farin cikin karrama mahaifinsa marigayi MKO Abiola da Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi a makon da ya gabata.
Idan ba a manta ba, shugaban Buhari ya karrama marigayi MKO Abiola da lambar yabo na girmamawa GCFR, sannan ya sauya ranar dimokradiyya a Najeriya zuwa ranar 12 ga watan Yuni.
A hira da yayi da gidan Talabijin na Channels, Kola ya yi kira da ayi watsi da kiran da majalisar tarayya ta yi cewa a matsa a sanar da sakamakon zaben mahaifin sa da ake ta cewa wai shine ya lashe zaben 1993 din.
“In banda surutu babu abin da ‘yan majalisa ke yi a zauren majalisar. Ko da ma sun nemi yin wani abu, da zarar sun mika ga kwamitin majalisar a nan take mutuwa murus.
Bayan haka Kola ya kara da cewa koda zabe ta zo cancanta za su bi, ” muna nan muna jiran ‘yan takaran da sauran jam’iyyun kasar nan zasu fitar. Daga nan za mu duba wanda ya fi dacewa da cancanta sai mu zaba.
Discussion about this post