Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON), ta bayyana kara wa’adin ranar da za ta rufe karbar cikon kudaden aikin Hajjin 2018.
Darakatan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, da Yada Labarai Sulaiman Usman ne ya bayyana haka, a cikin wata wasika da ya aika wa dukkan Sakatarorin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta jihohin kasar nan a ranar 24 Ga Mayu.
Ya ce hukumar za ta rufe karbar cikon kudin aikin hajji daga maniyyata a ranar 30 Ga Yuni.
Ya kuma gode wa dukkan sakatarorin jihohi na hukumar jin dadin Alahazai da shubaganni dabi daya.
Discussion about this post