GANGAMIN ZABEN APC: An soke ‘yan takara 19

0

Jam’iyyar APC ta soke ‘yan takarar mukamai daban-daban har su 19, a daidai lokacin da taron gangamin jam’iyyar na kasa ke kusantowa.

Kwamitin da Gwamnan Jihar Imo Rochas Okorocha ke shugabanta ne ya soke ‘yan takarar.

Ya kuma bayyana cewa wasu masu korafi su 18 sun rubuta kukan su ga kwamitin.

Rochas ya yi wannan bayani ne a lokacin da kwamitin sa ke wa manema labarai jawabi, inda ya ce an rubuto korafe-korafen ne a kan mukamin Sakataren Tsare-tsare da kuma wasu mukaman da suka hada da na Shugabar Matan Jam’iyya.

Ya ce amma har yanzu ba a karbi wani korafi a kan mukamin dan takarar shugabancin jam’iyya ba da dan takarar Sakataren Jam’iyya na Kasa.

“Idan aka yi wani korafi a kan wani dan takarar da muka rigaya muka tantance, to mu na da ikon tsayawa kan bakan mu na tantance shi, idan ba shi da wani aibi. Sannan kuma mu na da ikon soke tsayawar sa takara, idan muka ga cewa korafin da ake yi a kan sa mai ma’ana ne sosai.

“Kuma tabbas mun karfi korafe-korafen a kan wasu ‘yan takarar kowane mukamai, amma banda mukamin masu takarar shugaban jam’iyya na kasa da kuma sakataren jam’iyya na kasa.”

Sai dai kuma Darakta Janar na Muryar Najeriya (VON), kuma jigo a cikin jam’iyyar APC, Osita Okechukwu, ya ce Rochas Okorocha ba shi da ikon soke takarar kowane dan takara. Ya ce doka ko kundin jam’iyya bai baiwa kwamitin Rochas wannan karfin ikon ba.

Share.

game da Author