GANGAMIN APC: Sama da ‘yan takara 170 ke neman mukamai daban-daban

0

Sama da ‘yan takara 176 ne na mambobin jam’iyyar APC ke fafutikar neman hawa mukamai daban-daban a taron gangamin da jam’iyyar za ta yi a Abuja.

Shugaban kwamitin tantance ‘yan takara da tsare-tsare, Aminu Masari ne bayyana wa manema labarai haka a Abuja jiya Lahadi.

Gwamnan na Jihar Katsina ya kara da cewa sama da ‘yan takara 176 din nan kowa ya sayi fam na neman tsayawa takara a mukanin da kowa ke da muradin tsayawa.

Gangamin taron wanda APC za ta gudanar na kasa, a ranar 23 Ga Yuni, ta shar’anta cewa gindaya cewa za a yi tsarin shiyya-shiyya ne.

Ma’ana, an raba yankunan da kowane mukami zai fito.

Masari ya kuma jaddada cewa jam’iyyar APC za ta bi ka’dojin da jam’iyyar ta gindaya ba tare da jikarar komai ba.

Share.

game da Author