Babban Cif Joji na Tarayya, Walter Onnoghen, ya kara jaddada gargadi kan matsalar da kin bin umarnin kotu da gwamnati ke yi zai iya jefa kasar nan.
Onnoghen ya yi wannan gargadin ne a yayin da ya ke gabatar da wata lacca a kan harkokin Shari’a a Jami’ar Lagos jiya Alhamis.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Onnoghen na cewa kashe-kashen da ake yi a fadin kasar nan, duk ya munanta ne saboda gwamnatoci sun ki bin umarnin da kotu ta bayar kan wasu hukunce-hukunce a baya.
“Duk gwamnatin da ba ta bin umarnin kotu, to ta na jefa kasar nan cikin mummunan rikice ne. Sannan kuma ba wai bin doka da oda kawai ne hakkin da ke kan gwamnati ba. Akwai babban hakki na bin umarnin kotu.
Gwamnatin Buhari ta na kan sahun gaban kin bin umarnin kotu, an ga haka wajen kin sakin Sambo Dasuki, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da kuma Nnamdi Kanu.