Dubban ‘yan PDP sun koma APC a Jigawa

0

Gwamnan jihar jigawa Abubakar Badaru da takwarar sa gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari sun yi wa wasu dubban ‘yan jam’iyyar PDP da suka canza sheka zuwa jam’iyyar APC wankar maraba.

An yi wannan buki ne ranar Laraba a garin Dutse.

Idan ba a manta ba a kwanakin bayan ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ziyarci jihar domin kaddamar da ayyukan da gwamnan jihar ya yi.

A karshe shugaban jam’iyyar APC na jihar Jigawa Sani Kiri ya yaba wa jagoran wadanda suka canza shekar Ibrahim Aujara.

Share.

game da Author