Dole sai mun mai da hankali wajen gano bakin zaren idan ba haka za mu fada cikin mawuyacin hali a harkar Fina-Finan Hausa – Zaharadden Sani

0

A hira da PREMIUM TIMES ta yi da fitaccen dan wasan fina-finan Hausa kuma Furodusa a farfajiyar Kannywood, Zaharadden Sani, ya bayyana mana yadda farfajiyar ke a sannu-sannu neman ta fada halin kaka ni kayi saboda masifar ‘yan fashi teku’ wato ‘Piracy’.

Zaharadden ya koka kan yadda waddan dabi’a na ‘yan fashin teku ke neman ya dukusar da farfajiyar fina-finan Hausa.

” Ina so in gaya maka cewa tabbas idan fa ba’a yi wani abu akai ba toh ko Allah ya kiyaye zamu fada cikin tsaka mai wuya.

” Yanzu abin ya baci sai kaje kasuwa kaga babu sabbin fina-finai. Ko kuwa kaga an dade da fidda fim a Sinima amma shiru ba ka gan shi a CD ba. Toh babban dalilin kuwa shine maganan wadannan muggan Mutane. Basu da mutunci ko kadan. Da zarar an saki fim sai su je su buga shi iya yadda suke so su fara sai da shi naira 50 zuwa naira 100 a fim din da Furodusa ya kashe miliyoyin naira.

” Wani abin takaici ma shine har ta waya ana tura fim kan naira 20 naira 50. Saboda Allah da me wannan yayi kama?

” Sai kaga yanzu Ka kashe makudan kudi wajen shirya fim amma uwar kudin ma ta fito babu ballantana a ce wai har an samu riba.

” Yanzu haka kawai ba za ka fidda kudi ka kashe wa fim ba bayan kasan baza ka sami riba ba. Biyan jarumai ma ya zama sai a a hankali, Ko sai kayi kaffa- kaffa tukuna in ba haka ba kuwa ka kira wa kan ka ruwa. Kana gani kiri-kiri wani na kwankwadan romon wahalar ka saboda bala’in irin wadannan mutane.

Zaharadden ya kara da cewa ita kanta Sinima da suke nuna fim din abin dai sai a ahankali, domin ba kowa bane zai iya fidda kamar naira 1000 zuwa sama ya shiga kallon fim daya.

” Kaga shi Sinima yana da kyau sai dai masu kallon fina-finan mu da yawa ba za su iya biyan irin wannan kudi ba na shiga kallo abin sai kaga dakyar ko tanan ma ake fita.

” Abu daya da zai taimaka wa wannan farfajiya sannan ya ceto mu daga gangarawar da muke yi, shine fa a samu a giggina gidajen kallo masu saukin kudi da mai sai da ruwa, dan achaba, mai keke Napep zai iya shiga ya kalla da dan naira 100n sa. Kaga hakan zai taimaka wajen samun isar da fina-finan mu duk inda muka so ya isa kuma ba za a fadi ba.

” Amma tabbas idan ba haka muka yi ba toh fa kaico abin sai du’ai fa. Ba za ka iya sakin fim a CD ba kai kuma ga dukiyar a make a cikin fim din.

A karshe Zaharadden ya bayyana cewa mafi yawan su sun fara karkata zuwa yi wa tashoshin nuna finafinan ta satalat,inda sukan siya fim din idan yana kyau sannan ya cika sharuddan su su nuna a gidajen talabijin din su. Abin fa ya kai ga haka.

” Dole ne fa sai gwamnati da masu hali sun sa mana hannu wajen giggina irin kananan wuraren kallon fina-finan a fadin kasar nan idan dai ana so a sai nasara wadannan miyagun mutane da sannan muma mu sami riba a kan sana’ar mu.

Share.

game da Author