Darussa 5 daga shan kashin da Najeriya ta yi a hannun Croatia

0

Mafi yawan masu sha’awar kwallon kafa a Najeriya sun sa rai Kungiyar Super Eagles mai wakiltar kasar a Gasar Cin Kofin Duniya a Rasha, za ta tabuka abin kirki a wannan gasa ta shekarar 2018.

Tun daga irin kalar rigar ‘yan wasan, ganin irin kyan rigunan, da kuma tsadar kudaden da aka buga su a kasar waje, an rika tunanin cewa ‘yan wasan za su iya fidaa kitse a cikin garwashin wuta a kasar Rasha.

Sai dai kuma abin ba haka ya ke ba. Duk da cewa Super Eagles sun samu damar hayewa na farko tun a wasan farko idan har suka ci Croatia, hakan bai yiwu ba.

A cikin rukunin su tun da farko Argentina ta yi kunnen doki da kasar Iceland, wacce ta zo gasar a karon farko.

Sai dai kuma idan aka bi tarihi, Iceland ta kawo karfi, domin ita ce ta hana England da Turkey zuwa Gasar Cin Kofin Turai, wanda Portugal ta lashe a shekarar 2016.

PREMIUM TIMES ta yi nazarin wasu darussa 5 da ya kamata a koya ko kuma a dauka domin kauce wa sake daukar buhun kunya a wasa na gaba.

Ighalo Ba Kwararren Maciyin Kwallon Da Za A Iya Dogaro Da Shi Ba Ne

Yayin da jama’a da dama ke korafin dalilin da ya sa aka tafi gasar da dan wasan Kano Pillar, Junior Lokosa, to banza dai Lokosa ya ci kwallaye har 19 a wasanni 22 da ya yi a Kano Pillar.

Amma a yanzu Odion Ighalo ba shi da salo ko dabarar cin kwallaye. Rabon da ya ci wa Najeriya kwallo tun cikin 2017, wasan Najeriya da Kamaru.

Duk da cewa a ranar da Najeriya ta kara da Croatia ce ranar zagayowar haihuwar Ighalo, maimakon ya yi wata bajinta, sai ya kasa tabuka komai.

Girke Mikel A Tsakiya Babban Kuskure Ne

Tun zuwan Jose Mourinho kingiyar Chelsea ya girke Mikel Obi a tsakiya, inda aikin sa shi ne raba kwallaye ga maciya ‘yan gaba, da kuma tare kwallo ya rika haka saurin gajiyar da masu tsaron baya. Sai kuma karbo kwallo daga masu tsaron baya ya na raba wa maciya kwallo ‘yan gaba.

Ya kamata a irin wannan wasa a rika matsawa da Mikel a gaba, ya fi maida karfi wajen yawan samar wa ‘yan gaba kwallo a daidai wurin da ya kamata su rika jaraba auna kwallon a cikin raga. Wato ya taya su tsara dabarar jefa kwallo a raga, maimakon Mekel a matsayin sa na lamba 10, ya rika yawan komawa baya ya na maida karfi wajen taya ‘yan baya kare hare-hare.

Shi kan sa J.J Okocha haka ya fada, har ya ce har gara a bar Alex Owobi ya buga lambar da Mikel ya buga.

Ba Su Nuna Kuzarin Yin Nasara Kan Abokan Fama

Irin yanayin wasan da suka buga, ba kwallon cin nasara ba ne a babbar gasa kamar cin kofin duniya. Ya kamata su rika sa jiki, kai hare-hare ba-ji-ba-gani da kuma takura wa abokan fama a hana su saket.

Sun manta da cewa kusan dukkan ‘yan wasan Croatia ba kanwar lasa ba ne. Daga ‘yan Real Madrid, said an Barcelona, sai dan Juventus sai sauran ‘yan manyan kulob-kulob da ake gogayya da su a duniya. Wasa uku kenan Super Eagles ta buga a jere ba ta jefa kwallo ko daya ba.

An Tona Asirin Rashin Gogewar Masu Tsaron Bayan Najeriya

Wasan Najeriya da Crotia ya kara fallasa matsalar rashin gogewar ‘yan bayan Super Eagles. Dama ko a wasan sada zumunta da kasar Czech Republic sai da aka nuna hakan.

Kulob mai kwararrun ‘yan wasa irin su Lucas Modric da Mario Manzukic, bai kamata ana kyale irin su wadannan ‘yan wasa su na sarrafa kwallo yadda ran su ke so ba.

Sannan kuma bai ma kamata idan za a buga wa Nijeriya kwana a kyale irin su babu wanda ya yi masu katanga tsakanin su da kwallo ba.

Rashin Samun Nasara A Wasan Farko

Rabon da Najeriya ta yi nasara a wasan farko na cikin kofin duniya, tun cikin 1998, a Faransa, inda ta caskara Spain da ci 3:2. Kafin nan kuwa a karon ta na farkon zuwa gasar, Najeriya ta ci kasar Greece, ta yi nasara a kan ta.

Ya kamata Najeriya tashin farko ta fara tashi da giya lamba daya, ta daga da karfin ta.

Da fatan a wasan ta na gaba za ta yi nasara, ko ana ha-maza-ha-mata.

Share.

game da Author