Wani likita mai suna Daivi Bawa ya bayyana dalilan da ya sa mata suka fi maza kamuwa da cutar sanyi.
A bayanan da ya yi Bawa ya ce a halicce al’auran mace a bude yake sannan bashi da kariya kamar na namiji wanda hakan ya sa cututtuka ke saurin shiga jikin su.
A dalilin hakan ya sa yake kira ga mata da su dunga kare kansu ta hayar guje wa amfani da bayi mara tsafta, wanke gaban su da sabulu, fesa turare a gaban su domin yin hakan zai kare su daga kamuwa da cututtuka da ya hada da cutar sanyi.
Ya kuma ce yin hattara ga ‘ya mace ya zama dole musamman yadda wasu cututtuka na sanyi basu da magani.