Buhari ya saka hannu a dokar cin gashin kai ga kotunan jihohi da majalisun dokoki na jihohi

0

Daga yanzu kotunan jihohi da majalisun dokoki na jihohi za su fara cin gashin kan su ne ba tare da sun jira gwamna ya ya saka musu hannu ba wajen hadadar kudaden su.

Kotunan jihohi ba sai sun jira gwamna ya saka masu hannu ba.

Haka itama majalisar dokoki na jihohi, harkokin kudaden su ya dawo hannun su ba ruwan su da sai sun jira gwamna.

Mai ba shugaban kasa shawara kana hulda da majalisar Dattawa Ita Enang ne ya bayyana haka wa manema labarai.

Yace cin gashin kai zai rage kai ruwa rana da ake yi tsakanin majalisa, kotuna da gwamnonin jihohin su.

Share.

game da Author