Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya biyar

0

A wani harin kwanton-bauna, Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya biyar bayan da motar da suke ciki ta taka nakiyar da Boko Haram suka kafa a kan hanyar wucewar su.

Rundunar Tsaro ta sojojin kasar nan, ta ce abin ya faru ne a lokacin da batarilyar sojoji ta 271 ke wani gumurzu bayan da Boko Haram suka yi musu kwanton-bauna.

Kakakin Sojoji Texas Chukwu, ya ce amma sojojin sun samu nasarar kashe ‘yan Boko Haram da yawa yayin da wasu da dama kuma suka gudu da raunuka a jikin su.

Ya kara da cewa an ceto mutane uku a wata dirar mikiya da sojojin suka yi wa kauyukan Jaje, Angwa Audu, Manjo Ali, Dabu Wulkaro da Gori Jaji.

Ya ce wadanda aka ceto din su na karbar kulawa da kuma duba lafiyar su a hannun sojojinn kasar nan. Kuma nan gaba kadan za a damka su ga hannun hukumar da ta dace.

Share.

game da Author