BIDIYO: Kalli wakar da kungiyar musulmi ‘MURIC’ ta yi tir dashi

0

Kungiyar kare hakkin musulmai MURIC ta ba mawaki ‘Falz’ kwanaki bakwai ya janye wakar ‘This is Nigeria’ sa na ‘This is Nigeria’ ko kuma su kai shi gaban kuliya.

Kungiyar ta soke wannan waka ne tana mai cewa yi wa musulunci cin fuska ne a wakar inda ya nuna ‘yan mata na rawar fitsara sanye da hijabi da hakan ba shaidar arziki bane ga duk wani musulmi.

Muric ta bayyana cewa bayan yi wa musulunci izgilanci, wannan bidiyo na waka zai iya tada rikicin da ba za aiya shawo kan sa ba.

Cikin abin da ya kara tada wa musulmai hankali a wannan bidiyo shine nuna wani bafullatani da garayar sa amma ya jefar ya dauki adda ya sare kan wani mutum.

Kungiyar ta ce duk irin wadannan abubuwa basu dace ya yi su ba.

Sun bashi kwanaki 7 ya janye wannan bidiyo sannan a dakatar da ci gaba da nuna ta ko kuma su kai shi kotu.

Sai dai mawakin, wato ‘Falz’ da babban dan fitaccen lauyan nan ne Femi Falana ya ce sai dai fa a hadu a kotu amma ba zai cire wakar ba.

Share.

game da Author