Kungiyar Tawayen Biafra ta bayyana cewa ta dawo da shirye-shiryen ta na neman ballewa daga Najeriya a cikin ruwan-sanyi, wanda haramtacciyar kungiyar Biafra ta fara.
A kan haka ne IPOB ta ce tuni har ta buga kuri’un kada zaben jin ra’ayin jama’ar yankin ko su na so a balle ko a’a.
Ta ce ta buga zunzurutun katin jefa kuri’a har guda miliyan 40.
Kungiyar ta ce hakan na nufin irin shirin da suka yi na ficewa daga Najeriya dungurugum a cikin ruwan-sanyi.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa Kakakin IPOB mai suna Emma Powerful na cewa matakin farko na kada kuri’un jin ra’ayin jama’a zai fara ne a cikin 2018, sai dai kuma bai fadi ranar da za a fada din ba.
Ya ce idan lokaci ya zo, za a raba wa duk wani baligi wannan kuri’a a fadin yankunan birane, kauyuka da lunguna da sako-sako.
Nnamdi Kanu ne shugaban kungiyar, sai dai kuma tun daga ranar da sojoji suka yi wa gidan sa dirar-mikiya, ba a kara jin motsin sa ba.