Bani da iko kan jami’an tsaron dake aiki Zamfara, ban isa in sa ba ballantana in hana – Gwamna Yari

0

Gwamnan jihar Zamfara ya bayyana cewa a halin da yake ciki yanzu bashi da sauran iko kan yadda tsaro zai kasance a jihar Zamfara.

Yari ya ce a matsayin sa na gwamna, ba shi da ikon yadda jami’an tsaro za su gudanar da aiki a jihar Zamfara kamar yadda mutane suke dauka.

Ya ce gaba daya yanzu daga sama ake abin, ” Bani da iko kan jami’an tsaron jihar, sannan ban isa in ce ga inda za a yi ba gane da tsaron jihar Zamfara. Cewa da akeyi wai gwamna ne ke da ikon samar da tsaro a jiha. a Zamfara dai ba haka bane.

” Dole in fito in yi magana, in gaya wa mutanen jiha ta da Najeriya gaskiya. Damar da doka ta bani duk boge ce domin ba yadda zan sa ayi bane ake yi gane da abin da ya shafi tsaro a jiha ta.

” Da kuke gani na dinnan, bani da ikon cewa ayi ko a bari game da tsaron Zamfara, Ko kuma ace wai zan iya sawa ko in hana ballantana har wai in hukunta wani jami’in da ya saba doka a jihar ta, abin da ga sama akeyi ni ana fanko ne kawai.

Yari ya bayyana cewa kisan da ake yi a jihar ya zama abin yashin hankali da tsoro.

Jama’a kusani, bani da iko kan jami’an tsaron dake aiki a Zamfara, ban isa in sa ba ballantana in hana, daga sama ake komai. Ni ma Yari na zuba musu ido ne.

” Haka kawai a sati duda sai kaji an kashe mutane sama da 30 kuma idan ba a manta ba shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin a tabbata an fatattaki mutanen da ke aikata wannan mummunar aiki amma hakan har yanzu shiru kake ji.

Share.

game da Author