Ba muyi maraba da dawowar Mimiko LP ba, ya tsaya can a PDP – Jam’iyyar LP

0

Shugaban jam’iyyar Labour Party ta kasa Mike Omotosho, ya bayyana cewa jam’iyyar ba za ta yi maraba da dawowar tsohon gwamnan jihar Ondo Olusegun Mimiko, cewa tunda ya yi watsi da jam’iyyar a wancan lokaci ya koma PDP ya tsaya can, ba su bukatar sa a LP din yanzu.

Idan ba a manta ba Mimiko ya zama gwamnan jihar Ondo ne a inuwar jam’iyyar LP sai a 2015 ya tattara komatsansa ya koma PDP.

Yanzu kuma ya ga abin ba dadi ne ko ya dawo LP kuma. Ba za mu amince da haka ba, cewar Omotosho.

” Babban dalilin da ya sa Mimiko ya ke so ya dawo LP din shine domin yayi amfani da ma’aikata wajen gyara batacciyar mutuncin sa a siyasance amma ba don a more sa ba.”

” Yadda ya wulakanta jam’iyyar yayi watsi da ita haka a lokacin da take bukatar sa, muma yanzu bama bukatar sa. Ya tsaya can a PDP abin sa kawai.

Share.

game da Author