Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya koka kan yadda mutane ke kin bada gudunmawar jini da yake ta yawaita a kasar nan yanzu.
A bayanan da ya yi Adewole yace bada gudunmawar jini na taimakawa wurin ceto rayukan mutane musamman mata da yara kanana.
” Sai dai abin takaici ne yadda kashi 10 bisa 100 na mutanen kasar nan ne kawai ke bada gudunmawar jinin su kyauta, kashi 60 bisa 100 ko sai an biya su sannan kashi 30 su kan bada jini ne kawai idan wani na su na bukata.
Ya ce maza za su iya bada gudunmawar jininsu bayan duk watanin hudu sannan mata bayan watanin uku.
” Hakan zai taimaka wurin bunkasa karfin garkuwan jikkunan mutane matuka.”
A yanzu dai hukumar samar wa da adana jini na kasa na bukatan ledan jini akalla miliyan 1.8 domin ceto rayukan mutanen marasa lafiya a kasar nan.