Ba zan dauki nauyin ko wane dan takarar gwamna a jihar Nasarawa ba – Al-Makura

0

Gwamna Umar Al-Makura na Jihar Nasarawa, ya bayyana cewa ba zai dauki nauyin duk ma wani ko wane ne zai gaji kujerar sa ta gwamna a zaben 2019 ba.

Gwamnan ya yi wannan furuci a ranar Asabar a lokacin Manyan Sakatarorin jihar da kuma Shugabannin Kananan Hukumomi suka kai masa gaisuwar Sallah a lafiya, babban birnin jihar.

Ya ce duk da dai ba zai goyi bayan kowane dan takara ba, amma jihar Nasarawa na bukatar wanda idan ya hau zai dora daga inda gwamnatin sa ta tsaya.

“Amma idan ana maganar goyon baya ba daukar nauyi ba, to zan yi taka-tsantsan kafin na goyi bayan wanda zuciya ta ta kwanta da shi, ba tare da nuna son rai na ba. Don haka cancanta zan bi, ba son zuciya ba.

“Don haka sai an tankade kuma an tace masu takarar gwamna domin a samu mafi cancanta wajen tabbatar da ci gaba da jaddada zaman lafiya da ci gaban jihar Nasarawa.”

Daga nan sai ya hori shugabannin kananan hukumomi da su tabbatar su na yin tsantsani wajen tafiyar da dukiyar kananan hukumomin su.

Share.

game da Author