A wata sanarwa na kasar Saudi Arabiya ta fitar da yamman Alhamis, ta ce an ga watan Shawwal a kasar.
Hukumomin kasar sun sanar da gobe Juma’a ranar Idi.
Baya ga kasar Saudi an ga watan a kasar Qatar, Dubai, Turkiyya da Kasar Indonisia.
Gidan talabijin din Al-Jazeera ne ta ruwaito wannan labarin.
A kasa Najeriya, ana sa ran ganin watan a yau. Sai dai har yanzu ba a sanar da ganin watan ba.
Discussion about this post