Wasu mahara da ba san ko su wane ba, sun bindige tsohon dan takarar gwamnan jihar Akwa Ibom, Okon Iyanam har lahira.
An bindige shi jiya Laraba, a cikin otal din sa da ya gin aba da dadewa ba a Mowe, jihar Ogun.
Yayan mamacin mai suna Victor Iyanam, shi ne ya tabbatar da faruwar hakan a cikin wata takardar bayanin da ya fitar.
Victor, wanda shi ne tsohon antoni janar na jihar Akwa Ibom, ya ce Okon ya bude sabon otal ne na sa a Mowe, jigar Ogun, kwanan nan ba da dadewa ba, inda kusan a can ne ma ya fi zama, domin ya ga yadda al’amurra ke gudana.
Ya ce an harbe shi ne yayin daake wata dabdalar bikin murnar zagayowar ranar haihuwar wani, inda wasu ‘yan fashi da makami ko kuma ‘yan ku-kashe-a-biya-ku, suka yi wa wurin dirar mikiya, da misalin karfe 12: 30 na dare. Su na isa suka fara bude wuta.
“Da suka fara harbe-harbe, sai kuma suka tambayi wanda ke da otal din. Ko da suka gane shi sai kawai suka bude masa wuta nan take, kuma ya mutu a wurin.”
Jami’an ‘yan sanda sun tabbatar da kisan, kuma su ne ma suka kai gawar sa a dakin ajiyar gawa na asibitin garin.