Akwai ‘yan Najeriya 1500 tsare a gidajen kurkukun kasar Italiya – Jakada

0

Jakadan kasar Italy a Najeriya, Stefenou Ponteselli, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya da ke daure a gidajen kurkuku daban-daban a kasar ba za su rasa kai 1500 ba.

Ponteselli ya ce su na tsare ne sakamakon aikta laifuka daban-daban da suka yi, wanda ya kauce ko ya karya dokokin kasar Italiya.

Da ya ke ganawa da manema labarai ranar Litinin a Abuja, ya ce a gaskiyar magana adadin ya yi yawa sosai, kuma abin damuwa ne matuka.

“Sau da yawa kuma duk wanda ya kammala wa’adin zaman kurkuku, sai mu maido shi Najeriya, saboda ko sun ci gaba da zama, ba bin doka da oda su ke yi a kasar na Italiya ba.”

Sai dai kuma ya musanta cewa kasar Italiya ta na maida ‘yan Najeriya masu hijira zuwa a kasar zuwa cikin kasar Libya.

“Italy ba ta taba maida ko da dan Najeriya guda daya zuwa cikin kasar Libya ba. Wasu lokutan ‘yan Najeriya kan zauna cikin Libya ne, su kasa gaba su kasa yin baya, wato sun kasa komawa Najeriya, kuma sun kasa tsallaka ruwa su shiga Italy. Amma ba mu taba maida ko da dan Najeriya daya zuwa cikin Libya ba.”

Share.

game da Author