Abin da ya hana a gudanar da ayyukan raya kasa a Adamawa lokacin ina Mataimakin Shugaban Kasa -Atiku

0

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa rashin bai wa mataimakin shugaban kasa karfin ikon aiwatar da ayyukan raya kasa da dokar Najeriya ta yi, shi ne babban dalilin da ya sa a lokacin mulkin su ba a gudanar da ayyukan raya kasa a jihar Adamawa ba.

Atiku ya ce dokar Najeriya ta takaita ayyukan mataimakin shugaban kasa a cikin ofis kawai, sai fa wasu ayyukan wakilci idan shugaban kasa ya nada shi.

Da ya ke jawabi, Atiku ya ce ai ya na da ayyuka da ya tsara don kashin kan sa domin a yi wa jihar Adamawa, musamman ma da ya ke a matsayin gwamna a ka fara zaben sa, kafin a rantsar da shi ne, aka maida shi mataimakin shugaban kasa.

Ya ce duk da haka ya na da ayyukan da ya tsara domin a yi wa jihar a lokacin da ya zama mataimakin Olusegun Obasanjo.

A filin jirgin sama Fatakwal Atiku ya yi wa manema labarai wannan jawabi, a ci gaba da rangadin da ya ke yi a jihohin Bayelsa da Rivers, ya na tuntubar masu ruwa da tsaki, dangane da batun takarar sa ta shugabancin kasa a karkashin jam’iyyar PDP a 2019.

Ya kara tunatar da manema labarai cewa a matsayin aikin sa na mataimakin shugaban kasa, doka ba ta ba shi ikon gina ayyukan raya kasa ba, aikin sa shi ne na mataimaki, kuma kowa ya shaida irin kokarin da ya yi a matsayin sa na mataimaki.

Baya ga wannan kuma ya nuna takaicin cewa kitimirmirar siyasar da aka rika kitsawa a lokacin ta haifar da illa ga daukacin al’ummar jihar Adamawa, domin ta hana a ci gaba da yi wa jihar ayyukan raya kasa, saboda mugun halin wasu kusoshin Najeriya a lokacin.

Atiku ya ce a lokacin da suke kan mulki, har an bayar da kwangilar aikin titin da ya tashi daga Mayo Belwa-Jada-Ganye-Tango da Yola-Mubi-Maiduguri, kua an tsara za su dangana da sake titin har zuwa Mambilla.

Ya ce amma banbancin siyasa da tuggun da aka rika nuna masa ne ya sa aka dakatar da aikin kiri-kiri aka ma soke shi, saboda bambancin ra’ayin sa da wasu ‘yan miya ta yi zakin siyasa.

Daga nan sai ya ce karya ne kuma rashin adalci ne da har wasu marasa tunani ke cewa wai da kudin da ya kamata a yi ayyukan titin ne shi Atiku din ya gina jami’ar sa ta American University da ke Yola.

Ya tunatar da cewa kowa ya sani shi dama dan kasuwa ne tun ma kafin ya shiga siyasa. Don haka ya ce rashin adalci da kuma daukar alhaki ne da har wasu ke masa sharri cewa wai idan ya zama shugaba zai saci kudin kasa.

Ya ce shi a yanzu ya gode Allah, domin ya na da rufin asirin sa, kuma kasuwancin sa na tafiyar da ba zai sa ya bata rayuwar sa wajen ganin sai ya wawuri kudin gwamnati ba.

Share.

game da Author