Ma’aikatan hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA sun fara yajin aiki saboda kin cika musu alakwurran da hukumar ta dauka.
Shugaban manyan ma’aikata na hukumar (ASCSN) Justin Uche ya bayyana haka sannan ya kara da cewa kungiyar na kira da a tsige shugaban hukumar Mustafa Maihaja saboda rashin sanin makaman aiki da kwarewa.
” Tun da Maihaja ya zama shugaban hukumar a watan Afrilu 2017 hukumar NEMA bata aiwatar da aiyukkan agaji ba yadda ya kamata.”
A yanzu haka ofisoshin hukumar na nan garke da kwado
Bukatun da suke bukata sun hada da:
1. Muna kira da a horas da ma’aikatan hukumar sannan da yi wa wasu da yawa karin girma.
2. Hukumar ta dakatar da biyan ma’aikata alawus din su da (DTA) da wasu kudade da ya kamata ana biyan ma’aikatan hukumar.
3. Muna neman inganta wajen aikin mu da sannan a kawo mana kayan aiki.
4. Muna kira da a dawo mana da ma’aikatan da aka dakatar da har yanzu Maihaja din yayi burus da umarnin majalisar wakilai da adawo da su maza-maza.
Uche yace hukumar ta yi kunan uwar shegu da wasikun barazanar daukan mataki da kungiyar ta yi ta rubuta wa hukumar kan wadannan batutuwa.
” Sannan koda majalisan wakilai ta bukaci a yi sulhu tsakanin mu da shugaban hukumar watsi da wannan kira Maihaja ya yi ya kauce abin sa zuwa kasar Morocco.”
Hukumar NEMA ta ce bata da masaniya wai ma’aikatan ta sun fara yajin aiki cewa yin haka karya doka ce.
Hukumar ta bayyana cewa cikin bukatun da ma’aikatan ke nema hukumar ta fara tattauna yadda za ta iya biyan su duka domin har an kafa kwamiti domin haka.
A karshe hukumar ta yi kira ga ma’aikatan da su janye wannan yajin aiki maza-maza domin yin haka karya doka ne
Discussion about this post