Kamfanin GAVI zata ci gaba da tallafa wa Najeriya

0

Ministan kiwon lafiya Isaac Adewole ya bayyana cewa kamfanin sarrafa magunguna mai suna GAVI za ta ci gaba da tallafa wa Najeriya daga yanzu jar tsawon shekara 10 masu zuwa.

Za a fara amfana da wannan tallafi ne daga shekarar 2021 zuwa 2028.

Idan ba a manta ba a kwanakin baya ne Adewole ya sanar cewa tallafin da kasar ke samu daga kamfanin domin yin allurar rigakafi na gab da karewa.

Ya ce kuma ce a halin da ake ciki kasar nan ba za ta iya biyan kudaden da za a bukata don yi wa yaran kasar allurar rigakafi ba musamman yanzu da yawan yaran da basu yi ba ya karu matuka.

Bincike ya nuna cewa shekaru biyar da suka gabata yara 800,000 ne suka rasa rayukan su sanadiyyar rashin yin allurar rigakafi a kasar nan.

Adewole yace sanadiyyar haka ne kamfanin sarrafa magungunan ta amince ta tallafa wa kasar har na tsawon shekaru goma.

‘‘A lissafe Najeriya na bukatan dala biliyan 2.7 sannan GAVI ta dauki nauyin biyan dala biliyan 1.03 daga cikin kudin sannan gwamnati za ta biya sauran.”

Share.

game da Author