Hukumar karban haraji ta jihar Nasarawa ta kammala shiri tsaf domin yin gwanjon baburan da jami’an ta suka kwato wurin mutanen da suka karya doka shekaru biyu da suka wuce a jihar.
Jami’in hukumar Okpadabu Adamu ya bayyana haka wa manema labarai ranar Litini a garin Lafiya.
A bayanan da ya yi Adamu yace hukumar ta kwace wadannan babura ne daga mutanen da basa biyan harjin baburan su da kuma wadanda basu da cikakkun takardun mallakar abin hawa a jihar.
Ya ce bayan hukumar ta kwace wadannan babura ta ba masu shi damar zuwa su karbi abin su a ofishin hukumar shekaru biyu da suka wuce amma shuru kake ji.
” Bisa ga doka hukumar na da damar yin gwanjon baburan bayan watanni uku da karban su amma hukumar ta ba mutane har shekara biyu, amma basu ce komai a kai ba Kila don basu yi takardun ba.
A karshe Adamu ya yi kira ga mutane da suke da ababen hawa a jihar da su guji karya doka irin haka sannan wadanda baburan su ke ajiye a hannun hukumar za su iya zuwa don karba idan suka yi takardun su kafin a yi gwanjon.