Dan kunar bakin wake ya kashe jami’in sa kai daya harin Maiduguri

0

Mataimakin kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar Barno Wakil Maye ya bayyana cewa wani dan kunar bakin wake ya tada bam a shingen jami’an taro dake hanyar Baga a Maduguri inda ya kashe jami’in tsaro na sa kai ‘Civilian JTF’ daya.

Maye ya fadi haka ne a garin Maiduguri da yake zantawa da manema labari, sannan ya kara da cewa wasu mutane 4 sun sami rauni a harin.

” Tun daga nesa jami’in tsaron na sa kai ya hango wannan dan kunar bakin wake ya doso su. Daga nan ne fa ya nemi ya dakatar dashi daga isowa wajen su, shine fa ya tada bam din.

A karshe shugaban kungiyar ‘Civilian JTF’ Bello Danbatta ya tabbatar da faruwar abun inda ya bayyana cewa dan kunan bakin waken ya yi kokarin far wa wasu masallata ne da sallar dare a yankin.

Share.

game da Author