DAMUWA: Yadda matasa ke kashe kan su a duk sekon 40 a duniya

0

Kungiyar kula da kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta koka kan yadda matasa a duniya ke kashe kawunan su saboda kawai sun shiga wata damuwa.

Jami’in kungiyar Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa bincike ya nuna cikin sakan 40 a duk rana ana samun wani da ke kashe kan sa a fadin duniyar nan saboda kawai wai ya shiga wata damuwa.

Ya kara da cewa hakan babban matsala ce da ke sanadiyyar rayukan mutane da dama.

Ya ce da yawa hakan kan faru ne ko dai don rasa wani masoyi ko wani abu da ake muradin sa.

Yayi kira g akafafen yada labarai da su mai da hankali wajen fahimtar da mutane illar yin haka da kuma hanyoyin da za a iy bi domin gujewa fadawa cikin damuwa.

Share.

game da Author