Kotu dake Magajin Gari a jihar Kaduna ta gurfanar da wani mutumi dake kokarin yi wa wani kwacen matarsa.
Yusuf Sadi da ya shigar da karar a kotu ya bayyana cewa Abubakar Mustapha ya fara bibiyar matarsa Nusaiba bayan ta tafi gidan su wankan jego a Kafanchan.
” Tun da mata ta ta tafi gidan su wanka har yau ta ki dawo wa gida.
” Sannan a lokacin da na je duba ta da sabon jariri Mustapha ya yi barazanar la’anta ni saboda na bita har cikin dakin sa da taho garin.
Yusuf ya ce kwace ce ta karfi da yaji Mustapha yake su yayi masa, sannan ya na rokon kotu ta raba su ta dawo masa da matar sa.
Ko da yake Mustapha ya karyata Yusuf, Kotu ta mika sa ga ‘yan sanda domin ci gaba da bincike.