Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon mataimakin gwamnan jihar Bauchi Babayo Gamawa tare da wasu mutane biyar a babbar kotun jihar.
Hukumar ta gurfanar da wadannan mutane ne bayan zargin wasushe Naira miliyan 500 da suka yi a lokacin suna gwamnati.
Cikin wadanda hukumar EFCC ta guranar sun hada tsohon sakataren gwamnatin jihar Bauchi Ahmed Dandija da Aminu Hamayo, tsohon kwamishinan filaye Dahiru Madaki, babban mashawarcin tsohon gwamna Isa Yuguda kan al’amuran aikin Hajji Sanusi Sarkin -Aska, tsohon mamba a majalisar dokokin jihar Bauchi Aliyu Jallam.
Lauyan hukumar EFCC ya roki kotu da ware sunan Dandija daga cikin jerin sauran domin a fara yi yi musu shari’a.
Daga nan ne lauyan dake kare Dandija, Nasiru Malam ya ki amincewa da hakan cewa hukumar EFCC ta gurfanar da mutanen shida kan laifi daya amma ba biyar.
Malam ya ce Ahmed ya kasa zuwa kotun ne a wannan rana saboda bashi da lafiya.
Ya ce saboda wannan dalili yana rokon kotun da ta dakatar da shari’ar har sai Dandija ya dawo kafin ta fara gudanar da shari’a.
Sannan ya koka cewa Dandija bai ma samu takardar gayyatar ya bayyana a kotu ba har yanzu.
A karshe, alkalin kotun Muhammed Shitu ya amince da rokon lauyan sannan ya umurci rajistaran kotun da ya gaggauta aikawa Dandija da takardar gayyata kafin kotun ta sake zama.
Za a ci gaba shari’ar a ranar 25 ga watan Satumba.