Gini ya ruguje da ma’aikata a Zariya, uku sun rasu

0

Jami’in kungiyar ‘Red Cross’ a Zariya Jihar Kaduna Abdul-Muminu Adamu ya bayyana cewa mutane uku sun rasa ran su sannan wasu bakwai sun sami rauni sanadiyyar rushewar ginin wata makarantar Islamiyya a Unguwar Kaya.

Adamu ya ce wannan abu ya faru ne ranar Juma’a yayin da ma’aikatan gini ke kan aiki a wurin.

‘‘Wani cikin mutanen dake wurin ne ya rugo da gudu ya kira mu a daidai abin na faruwa, daga nan kuma mu ka falla a guje zuwa wajen ginin inda Allah ya bamu sa’an ceto mutane 7 cikin gini da gawar uku da suka rasu.

” Mun kai mutanen da suka sami rauni asibitin koyar wa na Jami’ar Ahmadu Abello dake Zariya.

A karshe shugaban hukumar bada agaji na jihar Kaduna Ben Kure da jami’in hukumar kashe gobara na jihar Paul Fedelix-Aboi sun yi kira ga mutane da su guji daukan ma’aikatan da basu kware ba a aikin gini a duk lokacin da za su yi gini.

Sun kuma ce za su ci gaba da aiki a wurin domin tabbatar da cewa sun zakulo duk wani da ginin ya dane.

Share.

game da Author