Bambanci tsakanin sukar ‘yan siyasa ga mahukunta da na miyagun Malamai, Daga Magajin Mallam

0

Siyasar Dimokradiyyar Najeriya ta yau ‘yan siyasa suna goyon baya ko sukan shugabanni gwargwadon yadda ake yi da su ko ba’a yi da su. Ma’ana sun mayad da ita sana’a wacce suke cin abinci da ita.

Zaka ga ‘yan koran ‘yan siyasa suna yabo da kare ubannin gidajen su na siyasa da yin suka da aibanta abokan gogayyan ubannin gidaken su na siyasa saboda dan abun hannu da suke samu ko fatan samu ba wai don Allah da kishin Al-Ummah ba.

Da wannan shugaban da suke suka da aibantawa zai jawo su a jiki ya ba su kudi masu tsoka ko mukami, za ka sha mamakin yadda cikin sauki za su zama bakin ganga (duk inda aka buga zaki).

Saboda haka za ka gane ‘yan siyasa hamayyarsu ta son rai ne mai wa’adi. Dalili kuwa shine, shugaban da suke zagi yau da zaran gobe ba shi ke mulki ba sun gama da shi, hasali ma zuwa wani dan lokaci idan suka fara sukan shugaba dake kan mulki su kan yabi wanda suka aibanta jiya, su ce yafi wanda yake kai yanzu zama alheri ga Al-Ummah.

Wannan ke tabbatar da cewa ‘yan siyasa duniyarsu kawai suke gwagwarmayar nema cikin yabo ko suka, babu ruwansu da me Addini ya tanadar game haka, saboda ba shine madubin dubawansu ba. Shi yasa kudi ko na namu-duka ne (na Al-Ummah) aka ba su za su karba su ce rabon su suke ci.

Amma miyagun Malamai su ne matsalar Al-Ummah gaba daya, suna siyasantar da Addini su bata tunanin mabiyan su da juya kwakwalwar su da sunan Addini. Sun bace su batar da mabiyansu.

Zaka ga ‘yan siyasa da ‘yan barandansu na goyon bayan mugun Malamin dake sukan abokan gogayyansu koda Akidarsu ta Addini ba daya ba ce. Idan da na su zai hau mulki gobe wannan mugun Malamin na jiya ya suki gwaninsu za su yi bara’a da shi.

Duk wani tada zaune da ya addabi jama’a a arewacin kasar nan tun daga ‘yan kungiyar Mai Tatsine, Boko Haram da Shia ta Zakzaky, tasirin miyagun Malamai ne a fafutukar kafa wata daula ta Musulunci da suke ikirari za ta zama mai adalci kuma samar da ita shine mafita, koda a sanadiyyar haka za’a rasa rayuka, dukiyoyi da samun rashin zama lafiya.

Sabanin ‘yan siyasa wadanda idan shugaba bai yi masu ba burinsu kawai shine su canza shi da wanda suke hasashen zai fi shi. Da wannan ne ‘yan siyasa basa gani kuma ba su damu da illar mugun Malami ba makutar zai taimakesu wurin cimma burinsu na siyasa.

A mahangar Musulunci samun shugaba nagari adali shine abunda ake so kuma Addini ya nunar. Akasin haka kuma jarabawa ce ga Al-Ummah, idan sun yi hakuri sun jure ya zama masu kaffarah, idan kuma suka ki, sai ya zama babu lada sai wahala kuma babu biyan bukata.

Babbar matsalar ita ce, tsarin siyasar Dmokradiyya ya bada dama kowane kare da doki zai iya neman shugabanci. Idan ka soki wannan, kila wanda zai biyo bayansa sai yafi wanda ka soka kafinsa.

Matukar ba za mu canza yadda muke zaban shugabanni daga matakin zartarwa zuwa wakilci ba, to har abada za mu ci gaba da jiya-i-yau, bara tafi bana. Domin kamar yadda musu iya magana ke cewa, “kowace gauta ja ce”.

Mafita kawai sai mun koma mun bi yadda aka zabi kalifufin Musulunci guda hudun nan (Abubakar, Umar, Usman da Ali Allah Ya yarda da su). Watau zabe bisa cancanta ta hanyar lura da wanda yafi nagarta a cikin mutane. Hausawa sun ce, “in ana dara fidda uwa ake”.

Duk wani mutumin kirki a unguwanninmu mun san su, amma bama tunanin tsamo su don su jagorance mu, mun bar mutanen banza a cikin harkar siyasa amma mun koma gefe muna aibanta su. Kamar mutumin da ya lazumci yin wankin kayansa da ruwa mai datti, sannan duk lokacin da kayan ba su fita sun yi haske ba ya yi ta korafi me ya hana su fita.

Matasa kuma idan suna so su yi tasiri a cikin harkar siyasa sai sun bar siyasar kudi kuma sun hana ‘yan uwansu matasa banga’ siyasa ta ingantattun hanyoyin wayar da kai da koya musu sana’o’i.

Allah Ya bamu ikon gyara, Yasa mu dace da abunda yake so kuma ya yarda da shi. Ameen

Magajin Mallam: Abu Yahya (Aslam)

Share.

game da Author