Zubar da ciki da ‘yan mata ke yi yanzu ya zama ruwan dare a kasar nan – Likita

0

Wani Likita a asibitin koyar wa na jami’ar Ilori kuma likitan mata mai suna Gboyega Fawole ya yi kira ga mata musamman ‘yan mata da su guji yawaita zubar da ciki cewa hakan na iya hanasu daunkan ciki nan gaba.

Fawole ya yi wannan kira ne da yake yin jawabi a taron da kungiyar addinin musulunci na ‘Islamic Missionaries Association Of Nigeria (IMAN) ta shirya a Ilori jihar Kwara.

Likitan ya ce ya gano cewa mafi yawan lokuta a asibitin da yake aiki ‘yan mata kan zo neman a cire musu ciki.

“Yawan zubar da ciki na da matukar illa ga mahaifar mace domin nan gaba ko da ta yi aure haihuwa sai ya iya gagaranta.”

Ya ce domin guje wa haka yake kira ga ‘yan mata da su guji yawan saduwa da maza har suna daukan ciki kafin su yi aure.

Ya kuma yi kira ga mata da su daina wanke gaban su da sabulu su kuma guji fesa turare domin hakan na iya cutar da lafiyar su.

” Idan budurwa ta ji wani iri-iri a jikinta ta gaggauta sanar da mahaifiyar ta.”

Share.

game da Author