Jami’an Kwastam sun kama manyan motoci tule da man fetir a iyakar Kamaru

0

Shugaban hukumar kwastam dake kula da shiyar Taraba da Adamawa Kamardeen Olumoh ya bayyana cewa sun kama tankunar mai a iyakar Najeriya da Kamaru ana kokarin fita da su ta bayan fage.

Olumoh ya fadi haka ne wa manema labarai ranar Alhamis a Yola.

Yace tankunan man na dauke da fetir da ya kai lita 20,550 a kauyen Sahuda dake kusa da iyakar Najeriya da Kamaru.

Olumoh yace domin kare shiyoyin sa daga fadawa cikin irin wannan mummunar hali hukumar ta kafa matakan tsaron da za su taimaka musu wurin dakile irie-iren wadannan masu yin fasakwaurin a iyakokin kasarnan.

Share.

game da Author